Takaddama tsakanin Talon da Tiani
May 9, 2024Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin ya ce sai Jamhuriyar Nijar ta bude iyakar kasarta don ci gaba da hada-hada kamar yadda take a baya, idan har tana son samun damar jigilar 'danyen man fetur dinta.
Karin bayani:Fitar da man Nijar ta Benin cikin gagari
Shugaba Talon ya bayyana cewa haka siddan Nijar ta rufe iyakarta da Benin ta hana shige-da-ficen kayayyaki ba tare da sanar da ita dalili ba, to amma da zarar Nijar din ta bude kan iyakarta, kuma suka daidaita al'amura a hukumance, to hakika nan take za ta bata damar safarar man fetur dinta.
karin bayani:'Yan bindiga sun halaka mutane a iyakar Jamhuriyar Benin da Nijar
Tun a cikin watan Fabarairun da ya gabata ne dai kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta janye takunkumin da ta kakabawa Jamhuriyar Nijar bisa dalilin juyin mulkin da sojoji suka yi gwamnatin dimukurodiyya ta Mohamed Bazoum, to amma Nijar bata amince da bude iyakarta da Benin ba.
Wannan dai wani nakasu ne ga yarjejeniyar hada-hadar man fetur din tsakanin Nijar da Chaina daga mahakar mai ta Agadem, da ta kai Dalar Amurka miliyan 400.