1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin addini a ƙasar Indiya

December 26, 2007
https://p.dw.com/p/CgRk

A ƙasar India an tura daruruwan yan sanda zuwa jihar Orissa dake gabacin kasar, kwana daya bayan mabiya addinin Hindu masu ra’ayin riƙau sun yi arangama da kristoci.Mutun guda ne ya rasa ransa wasu kuma su 24 suka jikata tun ɓarkewar fadan a ranar litini da ta gabata.Masu ra’ayin na rikau suna zargin kristocin da yunkurin jan hankali yan hindu da su rungumi addinin krista. Kristocin a nasu ɓagare sun ce waɗanda suka rungumi addinin sun yi murnan tsira daga tsarin addinin hindu.An kuma tura ƙarin yan sanda zuwa garin Goa wanda wuri ne na yawon shakatawa.Masu nuna adawarsu da aikin raya wannan wuri sun yi kira ga yan yawon shakatawa da su bar wurin nan da karshen wannan mako in ba haka su fuskanci zanga zanga.