Rikicin Amirka da Koriya ta Arewa
March 29, 2013Talla
Koriya ta Arewan dai ta ce mudin Amurka ta kai mata farmaki to ko shakka babu za ta maida martani ta hanyar kai harin ramuwar gayya a sansanonin sojin Amurkan da ke Koriya ta Kudu da Japan.A wata ganawa da ya yi da manyan hafsoshin sojin kasar, shugaban Koriya ta Arewan Kim Jong-un ya ce lokaci ya yi da za su rarrabe tsaki da tsaba da kasar ta Amirka.
Wannan shelar da Koriya ta Arewan ta yi dai ta biyo bayan shawagin da ta ce sojin Amurka sun yi a sararin samaniyar ta da jiragen yaki.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas