Rikicin aware na yankin Cashimire na Indiya
September 13, 2010Mutane 13 sun rasa rayukansu a yankin Cashimire na ƙasar Indiya a lokacin da musulmin ke ci gaba da tayar da ƙayar bayan da suka fara tun watanni ukun da suka gabata da nufin nuna adawa da manufofin gwamanti da ke ci a yanzu. wata majiyar 'yan sanda ta nunar da cewa keta wani shafin alƙur'ani mai tsarki da wasu tsirarun mutane suka yi a birnin Washington na Amirka ne ya haifar da haihawar ƙamarin a wannan yanki da musulmi ke da rinjaye.
A garuruwan Banpipora da kuma Pampore masu zanga-zangar suka fi rasa rayukansu bayan da 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsasu, tare da harbe-harben kan mai uwa da wabi. A wani mataki na neman kwantar da ƙurar rikicin da ya ɓarke a yakin na Cashimire, gwamnatin Indiya ta fara nazarin ɗage dokar ta ɓaci da ta kafa a wannan yankin tun shekaru 20 da suka gabata.
Mutane dubu 47 ne suka rasa rayukansu tun bayan da mazauna wannan yanki suka fara fafutukar ɓallewa daga ƙasar ta Indiya. Kashi biyu bisa uku na 'yan Cashimire ne ke neman yankin nasu ya zama ƙasa 'yantata, yayin da kashi ɗaya bisa uku kuma ke neman yankin ya haɗe da ƙasar Pakistan.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu