1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin bayan zabe a Mozambik ya hallaka mutane

Binta Aliyu Zurmi
November 9, 2024

Rahotanni daga Maputo babban birnin Mozambik na nuni da cewar adadin mutanen da suka rasa rayukansu tun bayan barkewar rikicin bayan zabe ya kai mutum 30.

https://p.dw.com/p/4mpDt
Mosambik Maputo 2024 | Proteste nach Wahlen
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Kasar da ke gabashin Afirka ta tsinci kanta ne a rikicin bayan zabe, bayan tabbatar da jam'iyya mai mulki ta Frelimo a matsayin wace ta yi nasara da gagarumin rinjye na sama da kaso 70 cikin 100 a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 9 ga watan Octoba.

Madugun adawa Vanancio Mondlane wanda ya sami kaso 20 cikin 100 na kuri'un da aka kada , ya ayyana zaben a matsayin wanda aka yi wa magudi da aringizon kuri'u.

Tun bayan barkewar boren jami'an tsaro ke amfani da hayaki mai sa hawaye da karnuka domin tarwatsa al'umma. Tuni kasashen da ke makwabtaka da Mozambik din suka fara daukar vmatakin rufe iyakokinsu a yunkurin hana shigar rikicin kasashensu. 

Karin Bayani: Afirka ta Kudu ta garkame iyakarta da Mozambik