1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 10 da fara rikicin Boko Haram a Najeriya

July 26, 2019

Ranar 26 ga watan Yuli 2009 an wayi gari a Maiduguri da jin harbe-harbe da ba su saba ji ba harkokin sun tsaya cak jami’an tsaro sun kai ruwa rana da ‘yan kungiyar da ake kira Yusufiyya ko ‘yan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/3Mmnz
Zahl der Toten in Nigeria höher als befürchtet
Hoto: picture-alliance / dpa

Wannan shi ne za a iya cewa ya haifar da rikicin Boko haram da aka kwashe shekaru 10 ana fama da shi wanda ya bazu zuwa wasu jihohin Najeriya da ma kasashen makobta kamar Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

Mutanen binnin Maiduguri sun ce ba za su taba mantawa da wannan rana saboda abin da suka shaida da ya ba su mamaki kuma ya tayar musu da hankali gami da sauya musu rayuwa baki daya. Da yawa dai ba su taba jin harbin bindiga ba sai a wannan lokacin inda wasu ba su taba ganin gawa a kasa a zube sai lokacin.

Polizeiposten in Nordnigeria
Hoto: Katrin Gänsler

Wasu da ma sun ce abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne yadda suna ji suna gani ake harbe mutane har lahira.

Babu shakka birnin Maiduguri ya shaida ganin keta hakkin dan Adam wanda ba su taba gani ba sai dai su ji labari ko kuma gani a fina-finai. Yayin da jami’an tsaro ke farautar ‘yan kungiyar Boko Haram suna harbe su a bainar jama’a, su ma ‘yan kungiyar haka suke farautar jami’an.

Bayan kwashe lokaci ana wannan hali dai sai kura ta lafa inda jami’an tsaro suka sanar da kame shugaban kungitar Malam Muhammad Yusuf. Wannan shi ne za a iya cewa ya haifar da rikicin Boko haram da aka kwashe shekaru 10 ana fama da shi wanda ya bazu zuwa wasu jihohin Najeriya da ma kasashen makobta kamar Chadi da Kamaru gami da Jamhuriyar Nijar.