Rikicin chadi da bankin duniya
April 19, 2006Tchad
Kamfanin dake daukar nauyin harkokin hakan mai a Chadi ,ya fara gudanar da wata tattaunawa da gwamnatin kasar akan barazanar rufe bututun mai,sakamakon sabadi dake tafiya tsakanin ta da Bankin duniya kann kudaden cinikin mai.Bayan arangama tsakanin mayakan adawa dana bangaren gwamnati a birnin Njameina a ranar alhamis data gabata,fadan daya kashe mutane 350,gwamnatin chadin ta sanar da rufe bututun man kasar dake tafiya kamaru,dake makwabtaka ,idan har bata samu kudaden cinikn mai na watanni 3 da baa biya ta ba.Gwamnatin chadin dai ta sanar da cewa tana bukatar wannan kudi ne domin samarwa jamian sojin ta kayan fada ,da zasu yaki yan adawa da suka dauki watanni shida suna fada a gabashin kasar,wanda take zargin sudan da ingizawa.Ministan albasrkatun mai Mahmat Hassan Nasser yace gwamnati zata sake waiwayen wannan kuduri nata,idan har bankin duniya ya dakatar da rufe asusun cinikin man chadin dake London,din kasar Britania.