1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICIN DA BBC TA SAMI KANTA A CIKI.

Yahaya Ahmed.February 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvm7
Akwai dai dalilai da yawa, da suka janyo abin da za a iya kira "tuntuße" da shugabannin BBCin suka yi. A cikin shekaru 25 da suka wuce, an sami sauyi da yawa a al'adun yada labaran da aka saba da su a kafar. Canje-canjen da gwamnatocin Birtaniya, kama daga lokacin Margaret Thatcher, zuwa John Major da Tony Blair, suka yi wa tsarin kafofi daban-daban na kasar, sun janyo kakkausar suka daga wasu jaridu masu bin ra'ayin juyin juya-hali. A hankali ma BBC ta shiga cikin sahun, wadannan kafofin sadaswan. Firamiya Margaret Thatcher ce dai farkon, shugaban gwamnatin Birtaniya da ta yunkuri yi wa kafar BBCin garambawul.

Manufar da BBCin ta sanya a gaba, ta kare `yancin fadar albarkacin baki, da kuma yada takaicin jama'a game da matakan gwamnati, sun sa ta yi tashe a cikin shekarun 1990. Tun da Tony Blair ya hau mulki ne dai kuma, kafofin yada labaran Birtaniyan suka yi ta rikici da Alistair Campbell, kakakin gwamnatin Blair din. A nasu ganin dai, ba a taßa yin wani kakakin gwamnati mai kokarin yaudar jama'a da manufofin hukuma a Birtaniya, kamar shi Campbell ba. Maneman labarai da yawa, a cikinsu kuwa har da Andrew Gilligan na BBC, na yi masa zaton jirkita rahotannin kungiyoyin leken asiri, ta yadda za su hujjanta afka wa Iraqi da yaki, da Birtaniya da Amirka suka yi. A daya ßangaren kuma, an sami canje-canje da yawa a fannin yada labarai a Birtaniyan a cikin shekaru 20 da suka wuce. An dai wayi gari, aka ga cewa gaggan `yan kasuwa a fannin yada labaran, kamarsu Rupert Murdoch ne, ke mallakar muhimman jaridu da tashoshin talabijin na kasar. Wadannan kuwa na yakan duk wani ra'ayin da bai dace da nasu ba, ko da ma za su jirkita labarai ne don su cim ma gurinsu.

Don tsayawa kafada da kafada a tsereriniyar yada labaran da jama'a ke son ji ne, BBC ta shiga bin salon sauran kafofin. A nan ne kuwa za a iya ganin babban kuskuren da ta yi. Ta sake salon yadan labaranta, tana bin misalan wasu kafofin, ba tare da bin diddigin labaran da ta samu don gano tushensu ba. Ta hakan ne kuwa Andrew Gilligan ya sami shiga BBCin.

Babban darektan BBCin a cikin shekarun 1990, John Birt, ne kuma ya yi wa kafar wata gagarumar kwaskwarima, inda ya sake duk tsoffin na'urorinta, ya maye gurbinsu da sabon fasar na ta DIGITAL, ya kuma fadada sassan yada labaran, har aka kafa tashoshin nan BBC Rediyo 5 da BBC News 24. Babu shakka, wasu daga cikin shugabannin kafar ta BBC ba su amince da duk manufofin John Birt ba. A nasu ganin dai, canje-canjen da yake yi, za su janyo rashin ingancin rahotannin da kafar ke yadawa, da kuma darajarsu. A wannan lokacin dai, an sallami ma'aikata da yawa masu adawa da shugaban. Wasu kuma, da kansu suka bar kafar.

Amma har ila yau dai, BBCin na daya daga cikin kafofin yada abaran da aka fi amincewa da labaransu a duniya bai daya. Idan ko sabbin shugabannin kafar da za a nada, na son su kare sauran darajar da take da ita, to dole ne su dau matakan kula da irin labaran da ma'aikatanta za su dinga yadawa nan gaba.

In ko hakan bai samu ba, to babu shakka, kwarjinin wannan tashar, wadda ta dade tana jagorancin duk kafofin yada labarai a duniya, zai dusashe.