1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kobani na shafar Turkiya

October 15, 2014

Gwamnatin Turkiya ta gabatar da wani kudiri a gaban majalisar dokokin kasar da zai kara baiwa jami'an tsaron kasar karfin iko a yayin gudanar da ayyukansu.

https://p.dw.com/p/1DW63
Hoto: Reuters/Osman Orsal

Wannan dai ya biyo bayan zanga-zangar nuna bacin rai dangane da kin daukar wani mataki daga bangaren gwamnati wajen kare garin Kobani, da Kurdawan Turkiyan suka yi domin nuna goyon bayansu ga 'yan uwansu na Kobanin da ke kan iyakar Siriya da Turkiyan bisa farmakin da suke fuskanta daga kungiyar IS ta masu kaifin kishin addini. Akallah mutane 34 ne suka hallaka yayin da wasu 360 suka jikkata a yayin zanga-zangar. A hannu guda kuma duk da yakin taron dangi a kan kungiyar IS din da Amirka ke jagoranta, kungiyar na ci gaba da fadada ayyukanta a garin na Kobani, a kokarin da take na kwace iko da garin baki daya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu