1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin makiyaya ya halaka mutane 170

Ramatu Garba Baba
December 12, 2017

An samu asarar rayukan mutane fiye da 170 a wani rikici da ya barke a tsakanin wasu makiyaya a arewacin kasar Sudan ta Kudu mai fama da yakin basasa na fiye da shekaru hudu.

https://p.dw.com/p/2pDIC
Flüchtlingslager Süd Sudan Süd Kordofan
Hoto: AP

Alkaluman mamatan ya ninka wanda aka fitar a baya kan rikicin da aka kwashi kwanaki ana yi, mahukuntan kasar sun ce rikicin ya barke ne a tsakanin makiyaya 'yan kabilar Dinka da Rup da kuma Pakam, baya ga asarar rai mutane fiye da dari sun sami rauni.

Gwamnati ta sanar da ayyana dokar ta baci a yankin, tare da tura sojoji don tabbatar da zaman lafiya acewar Ateny Wek Ateny kakakin fadar shugaban kasar. An dai dadde ana samun rikici a tsakanin makiyaya a Sudan ta Kudu tun bayan barkewar yakin basasa a shekarar 2013 da ya kuma daidaita kasar.