Rikicin nukiliyar ƙasar Japan
March 16, 2011Sarkin ƙasar Japan Akihito ya yiwa al'ummar ƙasar jawabin da ba safai dama yake yinsa ba, biyo bayan girgizar ƙasa da kuma ambaliyar ruwa ta tsunami da suka janyo mutuwa ko kuma ɓacewar kimanin mutane dubu 11, a yayin da aka tabbatar da cewar wasu dubu huɗu da 340 kuma sun mutu. Akihito ya ce ya damu matuƙa game da halin rashin tabbas na abubuwan da za su iya faruwa a tashar nukiliya ta ɗaya a Fukushima, wadda ke kan hanyar narƙewa bayan jerin abubuwan da suka tarwatse a wurin sakamakon gaza aikin na'urorin hana ɗaukar zafi.
Hakanan gobara ta sake tashi a tukunya ta uku da kuma ta huɗu dake tashar nukiliyar a Larabar nan (16.03.11). Akan hakane hukumomin ƙasar suka sauyawa ma'aikata a cibiyar mazauni saboda hatsarin dake tattare da mummunan yanayin da aka shiga. Tuni dai matsalar ta yi ta'asiri ga tattalin arziƙin ƙasar ta Japan, wanda shine na uku mafi girama a duniya, inda gwamnatin ƙasar ta yi ƙiyasin cewar ƙasar ta yi asarar sama da abinda yakai na kuɗi Euro miliyan dubu 128.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmad Tijani lawal