1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicin Senegal: Sall ya sanar da ranar zabe

March 7, 2024

Hukumomin Dakar sun sanar da 24 ga wannan wata na Maris da muke ciki a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a kasar Senegal.

https://p.dw.com/p/4dFSh
Shugaban Senagal Macky Sall a yayin da yake jawabi a Diamniadio kusa da Dakar.
Shugaban Senagal Macky Sall a yayin da yake jawabi a Diamniadio kusa da Dakar.Hoto: Seyllou/AFP

Shugaba Macky Sall shi ne ya sanar da ranar gudanar da zaben a yayin wani taron majalisar zartarwar kasar da aka gudanar a yammacin jiya Laraba, kazalika Sall ya kuma rusa majalisar zartarwar kasar tare da nada ministan cikin gidan Senegal Sidiki Kaba, a matsayin sabon Firaiminista.

Tsohon Firaiministan da ke kasancewa shalelen Macky Sall, kuma wanda yake son ya gaje shi Amadou Ba, zai maida hankali ne kan yakin neman zabe gabanin ranar da hukumomin kasar suka fitar.

Kasar Senegal ta fada rikici tun bayan da Sall ya dage zaben watan Fabrairu sakamakon wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba a ayyukan hukumar zaben kasar da hakan ya jefa kasar cikin wadi na tsaka mai wuya kama daga zanga-zanga da kuma matsin lamba daga ciki da wajen Senegal.