Rikicin Shugabanci a Afghanistan
Shekaru 17 bayan da shigar sojin Amirka, har yanzu Afghanistan na fama da tada kayar bayan masu tsaurin kishin addini. Hare-haren da suka kai bara na kara nuna irin karfin da suke da shi.
Kalubalen tsaro
Jerin hare-hare a shekarar 2018 da 2019 sun yi sanadin rasuwar daruruwan 'yan Afghanistan tare da jikkata wasu da dama. Hakan ya nuna irin kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta. Wannan yanayi ya jefa al'ummar kasar cikin damuwa kana hakan ya nuna gazawar hukumomin kasar wajen tabbatar da tsaro.
Jerin hare-hare ba kakkautawa
Hare-haren da Afghanistan ke fama da su sun sanya ta kasance a kanun labarai na kasa da kasa. Kungiyoyi kamar na Taliban da IS kan dauki alhakin hare-haren da ake kai wa kasar. Gwamnatin kasar tana fuskantar matsin lamba kan batun tabbatar da tsaro a kasar da kuma karbe iko da yankunan Afghanistan da ke hannun 'yan bindiga irin su Taliban.
Manyan hare-hare na shekara-shekara
A shekarar 2018 ce 'yan Taliban suak kaddamar da manyan hare-harensu na shekara, idan suka yi watsi da tayin sulhun da gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani ta yi musu. 'Yan bindiga da ke fafutuka wajen girka irin tsarinsu na shari'ar Islama a kasar sun ce hare-haren da suka kaddamar martani ne kan irin dabarun da sojojin Amirka suka yi amfani da su a 2017 wajen tilasta musu kan su hau teburin sulhu.
Manufofin Trump kan Afghanistan
Shugaban Amirka Donald Trump ya fidda sabbin dabaru na ganin an daidaita lamura a Afganistan a shekarar 2017, inda ya sha alwashin horas da dakarun kasar da basu shawarwari. Har wa yau Trump ya lashi takobin tallafawa Afghanistan din a yakin da suke da 'yan Taliban da kuma cigaba da barin sojin Amirka a kasar amma a 2019 ya sauya matsayi inda ya ce za janye sojin kasarsa.
Shirin wanzar da zaman lafiya
Duk da cewar Shugaba Ashraf Ghani ya mika goron gayyata na hawa teburin sulhu da 'yan Taliban ba tare da gindaya wasu sharudda ba a shekarar 2018, ya zuwa yanzu 'yan kungiyar ba su nuna wata sha'awa ba, hasalima cewa suka yi shirin wata kullalliya ce gwamnatin ke kokarin bijiro da ita.
Tallafin Pakistan
Pakistan na fuskantar matsin lamba daga Kabul da Washington kan ta daina bada mafaka ga 'yan bindigar da ake zargi da kai hari Afghanistan, sai dai Islamabad ta ce ba ta da hannu kan wannan lamari don irin yadda take taka birki ga 'yan bindiga ba zai bada dama ga 'yan Taliban su dau kasar a matsayin maboya ba. Kabul da Islamabad kan zargi juna dangane da batun baiwa 'yan ta'adda mafaka.
Rawar madugan yaki a rikicin Afghanistan
Baya ga 'yan Taliban, madugan yaki a Afghanistan na da karfin fada a ji a rikicin kasar. A bara, Hizb-i-Islami shugaban Gulbuddin Hekmatyar ya koma Kabul bayan shafe shekaru 20 yana gudun hijira inda ya shiga siyasa. A watan Satumba na 2016 gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniya da Hekmatyar cike da fata na sauran madugan yaki a kasar da ma 'yan bindiga za su yi sulhu da mahukuntan Kabul.
Gazawar gwamnati
Yayin da dabarwa ta rikon madafun iko ke ci gaba da kamari a Afghanistan, farin jinin Shugaba Ghani da kabuwarsa a kasar na ci gaba da ja baya. Batun cin hanci da ake da shi a gwamnatin kasar da kuma rashin jituwa a gwamnatin hadin kan kasa da Amirka ta tallafa a aka samu sun taimaka wajen dakushe kokarin gwamnatin na kawar da ta'addancin.