Rikicin Siriya da Mali sun kankane taron ƙungiyar OIC na bana
February 6, 2013An buɗe taron ƙungiyar ƙasashen Musulmai ta duniya wato OIC, a birnin Alƙahira. Babban jadawalin taron zai fi mai da hankalini kan ƙasashen Siriya da Mali, waɗanda yanzu haka ke fama da tashin hakanli. Taron ya samu halartan shugabannin ƙasashe 26 daga cikin ƙasashe 57 mambobin ƙungiyar. cikin shugabannin da suke halarta harda na Jamhuriyar Islama ta Iran, wato Mahmud Ahmadinejad, dakuma shugaban ƙasar Turkiya. Da yake jawabin buɗe taron shugaban ƙasar Sinigal Macky Sall, ya buƙaci mahalarta taron da su tallafawa ƙasar Mali ta samu yancin ta, bayan barazanar yan ta'adda waɗanda suka addabi al'ummar arewacin Mali. Shugaban ƙassar Masar Muhammed Mursi, shine zai karɓi shugabancin ƙungiyar ta OIC daga hannun Sinigal.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal
AFP