Rikicin siyasa a kasar Gambiya
January 19, 2017Talla
Hankula sun karkata zuwa kasar Gambiya sakamakon rikita-rikitar siyasar da kasar ke shirin tsintar kanta a ciki bayan da shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh ya bayyana aniyarsa ta yin kememe akan gadon mulki, a dai-dai lokacin da wa'adn mulkin nasa ke cika. A hannu guda kuma shugaban kasar mai jiran gado Adama Barrow ya garzaya zuwa kasar Senegal, inda ake sa ran za a rantsar da shi a ofishin jakadancin Gambiya da ke Dakar babban birnin kasar.