Rishin tabbas kan zaben shugaban kasa a Kenya
September 17, 2017Talla
Kwararru dai na nuna shakku kan lamarin idan aka dubi yadda fadace-fadace na siyasa da sauran rudanin da ake fuskanta da ke mayar da hannun agogo baya kan batun shirya zaben. A halin yanzu dai lokaci na ci gaba da kurewa, inda ta kamata 'yan kasar ta Kenya su koma ga runfunan zabe a ranar 17 ga watan Oktoba, bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben da ya gudana sabili da manyan kura-kuran da aka tafka a zaben da aka yi na ran takwas ga watan Augusta da ya gabata. Tuni dama 'yan adawar kasar suka ce za su kaurace wa zaben muddin dai aka ki aminta da bukatun da suka gabatar na gyara a hukumar zaben kasar, wadda har yanzu ba a cike gurbin wasu wakillanta da dama da suka yi murabus ba.