Federer ya yi ritaya daga tennis
September 24, 2022Shahararren dan wasan kwallon tennis Roger Federer ya sanar da yin ritaya inda ya yi bankwana karshe da wasan da ya azurta shi tare da fito da shi a idon duniya. Dan shekaru arba'in da daya da haihuwan, ya yi wasansa na karshe a jiya Juma'a a gasar Laver Cup da ta gudana a Landan, inda shi da abokin hamayyarsa Rafael Nadal suka buga wasan mutum biyu-biyu da Frances Tiafoe da Jack Sock.
Dan asalin kasar Switzerland din na hawaye a lokacin da yi jawabinsa na karshe ga masu kallon da suka cika filin wasan domin yin bankwannan karshe ga gwaninsu. A dai bara a yayin gasar Wimbledon, fitaccen dan wasan ya fice daga gasar bayan da Hubert Hurkacz ya doke shi a zagayen kusa dana karshe, kafin nan, ya sha fama da ciwon gwiwa da ya hana shi sukunin buga kwallon. Federer ya lashe gasar Grand Slam sau ashirin a tarihi kuma ya buga wasanni sama da 1,500 a cikin tsawon shekaru ashirin da hudu, ya ce, shekaru sun ja wanda ya tilasta masa hakura da kwallon na tennis.