Hanyar isar da sakon matasalolin mutane
June 16, 2021Wani matashi a jihar Sokoto da ke Najeriya da ya kammala digirin sa a fannin kimiyar siyasa ya zabi ya soma aikin rubuce-rubuce don zakulo matsalolin da ke damun al'umma ya isar dasu ta hanyar rubutu ko faya-fayan Video da manufar shugabanni su gani don magance matsalolin.
Shi dai wannan matashi mai cikakken suna Abdulmumin Lawal Mande da akafi sani accidental poet ta bangaren rubuce-rubucen sa, yace ya shafe sama da shekaru hudu zuwa biyar yana gudanar da wannan rubuce-rubuce musamman ma wajen zakulo matsalolin dake damun al'umma ya kuma bayyana su ta hanyara rubutu. Matashin Abdul yayi bayanin yadda karon farko abunda ya ja hankalin sa har ya tsinci kansa cikin wannan aikin rubuce-rubuce
Koda yake matashi Abdul ya bayyana irin kalubale da kuma nasarori dake tattare a cikin wannan rubuce-rubuce da ya shafe dogon lokaci yana gudanarwa. Matashin dai yace yanzu haka yana horar da matasa dubarun salon rubuta don su fahimci sanin yadda zasu isar da sako ta hanyar alkalami.