Rufe sansanin Moria ya fito da matsalolin ‘yan gudun hijira
Lokacin da sansanin yan gudun hijira mafi girma a Turai ya kone yan gudun hijira a tsibirin Lesbos a Girka dole suka rika kwana a tituna ba tare da abinci ko ruwan sha ba. Marianna Karakoulaki ta nuna halin da suka shiga
Nauyi mai yawa
Moria, sansanin yan gudun hijira mafi girma a Turai yana dauke da mutane 12,000. Bayan da ya kone, yawancin 'yan gudun hijira sun bazama titunan Lesbos. Ba a bar su sun shiga babban sansanin Kara Tepe ba, maimakon haka sun yi wa kansu matsugunin wucin gadi da bukoki. 'Yan sanda sun killace su a bakin titi yayin da gwamnatin Girka ta gaggauta samar musu da sabon sansani na wucin gadi.
'Ba abinci mu ke bukata ba'
Bayan kwanaki na kwanan titi a gaban Kara Tepe, yan gudun hijirar sun yi zanga zangar lumana tare domin jan hankalin mahukunta su saurari bukatunsu. Yawancin yan gudun hijirar suna tsoron komawa wani sansani makamancin Moria. “Ba ma bukatar abinci”, yanci muke so, 'yan gudun hijirar suka shaidawa DW. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun baiyana sansanin Moria tamkar gidan yari budadde.
Karfin tasirin zanga-zanga
Daruruwan 'yan gudun hijira da ba za a kai su wani sansani mai kama da na Moria ba. Gwamnatin Girka ta mayar da martini da tura bataliya goma ta 'yan sanda da motoci biyu masu feshin ruwan zafi da tankokin biyu na sojoji zuwa sansanin wucin gadi da suka kafa a gaban sansanin Kara Tepe. An jefa hayaki mai sa hawaye a wasu zanga-zangar. Shin ya ma dace su yi zanga-zangar? Ga abin da wani ke cewa
'A ba mu 'yanci'
Mutum da kungiyar duniya. Muna bukatar ruwa, babu abinci a bamu ‘yanci” alamar da aka rubuta a kwali da turanci da kuma Dari da wannan yarinyar ‘yar Afghanistan ta ke rike da shi. Yawancin yan gudun hijirar suna zanga zangar adawa da rashin kyawun yanayi a kasashe ko yankunan da ake fama da rikici da suka hada da Afghanistan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo.
Babu abin da ya ke dawwamamme fiye da wucin gadi
Gwamnatin Girka ta ce sabbon sansanin yan gudun hijirar na wucin gadi ne. Amma wasu yan gudun hijirar da suka shafe fiye da shekara daya a sansanin Girka suna fargabar yana iya zama wani wurin jira da babu iyaka.
Babu mafita a kusa
Mako guda bayan gobarar Moria, yan gudun hijira suna na killace akan tituna. Jami’an gwamnatin Girka sun ce za a gaggauta mayar da mutanen zuwa sabon sansanin. Sai dai zuwa ranar Talata mutane 1000 ne kawai akan mayar zuwa wurin.
Rayuwar iyali a tsananin kunci
Yan gudun hijira sun jure wa tsananani. Bayan kwanaki na yunwa da kishin ruwa, yan gudun hijirar sun fara karbar tallafi. Robobi biyu na ruwa da kuma abinci. To amma da tsananin rana a watan Satumba a Lesbos, wasu na nuna bukatar a mayar da hankali kan tsafta musamman da annobar Covid 19. A kalla yan gudun hijira 31 da suka koma sabon sansanin sun kamu da cutar.
Idan rana ta fadi
Dare na tattare da hadari da fargaba ga 'yan gudun hijira wadanda ke zaune a tantuna a gefen hanya. Shin ka san yadda ake ji kwana a tsakanin maza da yawa musamman ga ‘ya mace matashiya? Shiga daji ko inda tantuna suke ko zuwa ban daki? Ba na iya bacci saboda ina tsoron kwari za su ciji ‘yata da kuma mijina, kamar yadda wata matashiya ‘yar Afghanistan da shaidawa DW.
'Allah ka taimake mu'
Rayuwa a sansanin Moria yana da hadari. 'Yan gudun hijira da dama sun fidda tsammani. Kasancewar sun bar gidajensu, sansanin gobarar da ta tashi a sansanin Moria ta tilasta musu kaura domin tsira da rayuwarsu. Bayan faduwar rana gomman mata da maza da yara kanana su kan hadu a kofar wani shagon burodi suna rokon Allah ya ba su sa’a a saurare su. Wasu suna kuka.
Zubar da hawaye saboda rashin makoma
'Yan gudun hijira da dama a Girka sun dandana kudarsu, bayan barin fagen yaki da kuma talauci. Ba mu zo nan domin karbar kudi ba. Ba mu zo nan domin sharholiya ba. Abin da muke bukata kawai shi ne ‘ya’yanmu su sami makoma mai kyau da kuma ilimi a cewar wannan mutumin dan Afghanistan kamar yadda shaida wa DW yana kuka yana zubar da hawaye.