1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta gagari sojojin yankin tafkin Chadi

July 7, 2020

Masana tsaro a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su kan rahoton da kungiyar da ke nazari kan rigingimu, International Crisis Group ta fitar wanda ke nuna gazawar rundunar kasashen yankin tafkin Chadi.

https://p.dw.com/p/3euou
Tschad Militär
Hoto: JEAN LIOU/AFP/Getty Images

Rikicin Boko Haram da aka faro a Najeriya shekaru 11 da su ka shude ya bazu zuwa kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, inda ya haifar da gagarumar matsalar tsaro da ta tilasta kasashen samar da wata runduna ta hadaka da nufin kawo karshen rikicin da ya lamushe dubban rayukan al’umma.

Mayakan Boko Haram na sake komawa a wuraren daga inda aka kore su
Tun lokacin da aka kafa wannan runduna shekaru shida da su ka shude ake fatan samun nasarar murkushe duk wasu masu gwagwarmaya da makamai a kasashen da ke bakin gabar tafkin Chadi da suka mamaye wurare da dama a wadannan kasashen.
Sai dai a cewar rahoton kungiyar da ke nazari kan rigingimu da ake fama da su a duniya International Crisis Group rundunar ba ta cimma nasarorin da ake bukata ba don kuwa duk da cewar suna fatattakar mayakan Boko Haram, amma mayakan na sake komawa wuraren tare da kai hare-hare har da hallaka jami’an tsaro da fararen hula.

Boko Haram
Hoto: Java

Rashin kudi da kayan aiki na zaman babban cikas ga rundunar

Tschadische Soldaten bei Rückkehr aus Mali 13.05.2013 mit Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Rahoton ya zayyana matsaloli da dama da suka hada da rashin kudade da kayan aiki da kuma rashin musayar bayanai na sirri tsakanin kasashen inda kuma kasashen ke mayar da hankali wajen yin yaki a rarrabe maimakon hada kai, abin da ake ganin shi ne tarnaki. Dangane da rashin hadin kai ko kuma rashin daukar mataki irin na bai daya Dr Kole Shatima na cibiyar raya dimukaradiyya  ya ce wannan babbar matsala ce da ke samar da gibi a wanann yaki.

Sai gwamnatocin kasashen yankin tafkin Chadin sun hada kawunan su 

Nigeria Tschadsee Konferenz
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a hannun hangun Idriss Deby na Chadi a tsakiya sai Muhammadu Buhari na Najeriya a hannun damaHoto: State House, Abuja

Rahoton Kungiyar dai ya nuna cewar matukar ana son samun nasarar wannan runduna to dole sai gwamnmatocin sun hada kai tare da neman tallafi kudade ko kayan aiki daga tarayyar Turai da kuma tarayyar Afirka. Gami da tabbatar da yin musayar bayanai na tsaro da kuma samo wasu hanyoyin na magance matsalar take hakkin jama'a da ake ganin shi ne ya haifar da nakaso kan samun kyakyawar dangantaka tsakanin al’ummomi da jami’an tsaro.