Rushewar garin Kobani
Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Kobani, wani dan jarida ya samu nasarar kutsa kai zuwa filin daga domin ya ganewa idanunsa yadda garin ya lalace sakamakon yakin, musamman bangaren da ke cikin Siriya.
Mutuwa da rushewa
Wani hari da aka kai da mota kirar Trela makare da abubuwa masu fashewa da manyan makamai ya yi sanadiyar rushewar dandalin Al-Salam da ke garin na Kobani.
Fashewar bama-bamai
Tukunyar nakiya da bata kai ga fashewa ba a tsakiyar barakuzan gine-gine a kan wata hanya da ke tsakiyar garin Kobani. Fadan da aka kwashe tsahon wata guda ana fafatawa tsakanin mayakan Kurdawa da 'yan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, ya rusa sassa masu yawa na birnin.
Hutu a filin daga
Daya daga cikin kwamandojin mayakan Kurdawa na YPG a Kobani, daya daga cikin rundunonin dakarun kabilun Kurdawa da ke yakar kungiyar ta IS.
Tsakiyar dandalin da aka ruguza
Daya daga cikin dakarun Kurdawa na duba yadda dandalin Al-Salam na garin Kobani ya daidaice.
Kadan daga cikin ginin da ya saura
Wani bangare na ginin wani gida a dandalin Al-Salam na garin Kobani da barin bama-bamai ya ruguza.
An cimma nasara?
Daya daga cikin mayakan Kurdawa ya dawo daga filin daga.
Ruguzawa da tagayyara
Hare-haren da 'yan ta'addan IS ke kaiwa a yankunan Kurdawa ya rusa kusan rabin babbar kasuwar garin Kobani.
Karfin zuciya da Jajircewa
Daya daga cikin mata mayakan dakarun Kurdawa na YPG a kan hanyarta zuwa filin daga. Mata masu yawa na shiga domin fafatawa a yakin da ake da 'yan kungiyar IS.
Tallafi daga sama
Hare-haren da Amirka ke kaiwa ta sama ya fara haifar da da mai idanu. Akalla ya taimaka wajen dakile nasarar da kungiyar ta IS ke samu a yakin kwace iko a garin na Kobani.