Najeriya: Matsalar rushewar gine-gine
November 2, 2021Sai dai 'yan uwan wadandan abin ya shafa na korafin tafiyar hawainiya na aikin ceto sauran mutanen, koda yake wasu na yabawa da irin kokarin da a ganinsu jami'an ke yi na ceto wadanda suka makale cikin barakuzan ginin da kuma ke da sauran ransu. Wani babban jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce ma'aikatan agaji na ci gaba da aiki tukuru domin ganin an zakulo sauran mutanen da ke karkashin ginin.
Al'ummar jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriyar dai, ta tsinci kai cikin rudani sakamakon wannan ibtila'in. Koda a shekara ta 2019 ma dai an samu afkuwar irin wannan ibtila'in, inda wani dogon benen ya fada kan wata makaranta tare da kashe dalibai kimanin 20 da kuma jikkata wasu da dama. Hukumomi a Najeriyar na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.