Sabani kan taron magance rikicin Siriya
January 20, 2014Talla
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya gayyaci kasar Iran zuwa taron neman magance rikicin kasar Siriya, da zai gudana a wannan mako a kasar Switzerland. Ban, ya nunar da cewa akwai rawar da Iran za ta iya takawa wajen warware matsalar.
A cikin martanin da ta mayar, babbar kungiyar 'yan tawayen Siriya, ta yi barazanar janyewa daga zuwa taron idan ba a janye wannan gayyata ba. Kasar ta Iran ta kasance babbar mai dasawa da gwamnatin Siriya ta Bashar al-Assad. Kasar Amirka tana cikin masu adawa da zuwan Iran zauren taron.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh