Sabbin dabarun gidaje na kare muhalli
May 31, 2017A yayin da wasu kabilu musaman makiyaya a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar ke amfani da sayoyin itatuwa wajen girka gidajen shiga da hakan ke taimakawa wajen fuskantar barazanar gurgusowar Hamada wace ke binne rijiyoyi da tabakunan baruwan bisashe a filayen
kiwo, Ganin yadda matsalar ke ci gaba da daukan wani sabon salo tare da saka makiyaya cikin zullumi, wani matashi da ya fito daga kabilar Abzinawa makiyaya da wannan matsala ta addaba ya bullo da sabin dubarun girka gidajen shiga na makiyaya ba tare da an yi amfani da
itace ba. Tuni dai shirin ya fara samun karbuwa ga makiyayan da ke zaman daji da kuma rugage.
Maman Mutari Alhaji Dodo shi ne matashin da ya kirkiro wanan fusaha ta kandagarkin yaki da hamada ta hanyar girka gidajen makiyaya da karafa sabanin sayoyin itatuwa da makiyayan ke amfani da su kan taimaki hamada mamayar jama'a.
Haruna Silimane na daga cikin kabilar Abzinawa makiyaya da suka gadi zama a rugage game da wanan fasaha cewa ya yi bayan Abzinawa makiyaya, har makiyaya 'yan kabilar Barebari daga gundumar Tesker ta bakin Ciroma Lawan daga rijiyar Aborak yabawa suka yi da fusahar.