1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin dubarun noman zuma a Kenya

Julia Mielke/ Kamaluddeen SaniDecember 30, 2015

Khole Kalume na daya daga cikin manoman zuman wanda kuma ya sami horaswa ta musamman a kan zuman wanda ya haifar masa da karin shigar kudade.

https://p.dw.com/p/1HViv
Kenia Wildhonig
Hoto: DW

Khole Kalume yayi girmansa ne da mu'amala da zuma kana kuma yana matukar kaunarsu. Daukacin danginsa sun yi dumu-damu da harkokin samar da zuma a tsawon lokuta. Shi a karan kansa yana da zuma akalla dubu 70 da ke da gidagensu 17 a kusa da kauyensu a kasar Kenya. Yanzu haka dai ya kan sai da zuma a kulli yaumin. Kalume na matukar alfahari da irin aikin da yake kuma a cewarsa yana amfani da hayaki ne wajen kula da zumansa.

"Kafin yanzu ina amfani da wuta ne wato wutar daji a yayin da muka sami horo daga cibiyar bayar da horaswa ta Kwetu. A nan ne na samu ilimin nakaltar yadda zan kula da kuma alkinta zuma na."

Horon da Kalume dai ya samu ya tafi sumul kalau tare da samun nasara kamar yadda aka tsara.

Harkar noman zuma ta bunkasa

Ba tare da jimawa ba ne dai a 'yan shekaru kalilan zuman da Kalume yake samu ya ninka yana kuma ajiye gidajen zuman da ya tanada a kusa da kauyensa a yayin da bishiyoyi ke fita kamar me a shekara. To amma mai bashi horaswar ya fada masa cewar a wannan da'irar bishiyoyin, zuma ba ya iya rasa abin kalaci.

Kenia Wildhonig
Hoto: DW

Kalume dai na daya daga cikin manoman zuma 20 da ke a kauyan Watamu da suka sami horonsu daga Emmanuel Kalama jami'i a cibiyar Kwetu. Shi kansa mai basu horaswar na da zuman nasa na kansa kuma ya fara wannan harkar ce tun shekaru goma da suka gabata.

"Muna koya musu yadda za su tanana zuma ta yadda za su kare bacewarsa daga doran kasa, kana kuma zuma yana da matukar mahimmanci sabili da yana taimaka wa mutane wajen zama abinci."

Jan aiki ne ajiye zuma

Ta yin haka ne ya janyo Khole Kalume shiga harkokin zuma tsundum kuma bai gane irin mahimmancin da ke tattare da noman zuman ba har su ragowar 'yan Kenyan. To amma ajiye zuma aiki ne ja sai dai kowa ya ci ladan kuturu ya biya kudin askinsa.

Kenia Wildhonig
Hoto: DW

"Burina shi ne na nakalci yadda zuma yake. To amma mafi yawan mutane sai su sakar maka da gwiwa ta hanyar cewar idan ka koyi yadda za ka yi nomansa babu kasuwar sam-sam a Kenya."

Kalume na sayar da lita guda ta zuma a kan farashin Euro 10 kana kuma ya sanya ribar da ya samu a cikin harkokin kiwon zuman. Kazalika yana fara amfani da wasu sinadarai don samar da nau'in kendiri.

"Ana samu sosai a harkokin kiwon zuma sabida za a iya harhada kayayyaki daban-daban."

Masu kiwan zuman dai suna da jan aiki a gabansu wajen janyo hankulan mutane da masu hulda da su rungumar harkar domin akwai riba a cikinta.