1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sabbin coci-coci a manyan hanyoyin Jamus

April 20, 2019

A Jamus yayin da majami'u ko coci-coci a cikin garuruwa ke kara yin karanci wasu kuma ke rufewa a waje guda ana samun karuwar mujami'un a wajen gari musamman a gefen manyan hanyoyi tsakanin garuruwa ko kasashe.

https://p.dw.com/p/3H60W
Autobahnkirche Thüringer Tor Süd
Hoto: DW/Maksim Nelioubin

A nan Jamus yayin da majami'u ko coci-coci a cikin garuruwa ke kara yin karanci wasu kuma ke rufewa a waje guda ana samun karuwar mujami'un a wajen gari musamman a gefen manyan hanyoyi tsakanin garuruwa ko kasashe. Wadannan mujami'u ko cocic coci suna debe wa matafiya kewa inda suke yada zango domin yin addu'oi ta neman waraka da yayewar bala'oi da cigaba a harkokinsu na rayuwa ko sana'a.

Maziyarta coci cocin na kan manyan tituna kan duba inda za su yada zango domin hutu bayan tafiya ta tsawon lokaci. Mujami'un na zama mahada ta al'umomi da dariku mabanbanta. Daya daga cikin wadannan wuraren ibada shi ne wanda ke kan babbar hanyar.

Autobahnkirche A4 Gelmeroda
Hoto: picture-alliance/dpa

Yawancin wadanda suka halarci mujami'ar na baiyana gamsuwa inda ma wasu ke alkawarin sake komawa idan tafiya ta bi da su ta hanyar. A daura da cocin a kan sami gidan mai da masu ababen hawa da masauki ko otel da kuma kanti.

A yanzu dai ana samun karuwar mutane da ke ziyartar mujami'u na kan hanya. Kiyasi ya nuna a kowace shekara akalla mutane miliyan daya ke tafiya akan hanyoyi daga gari zuwa gari. Cocin farko na kan hanya da aka gina a Jamus an yi shi ne a shekarar 1958 akan titin zuwa jihar Bavaria domin bai wa matafiya damar yin ibada a lokacin da suke tafiya a ababen hawa. Mujami'u sun karu zuwa 47. Haka kuma ana samun yaduwar irin wadannan wuraren ibada na kan hanyoyi a kasashen Ostiriya da Switzerland.