1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babi a dangatakar Indiya da Pakistan

July 27, 2011

Indiya da Pakistan sun buɗe sabon babi a dangatakarsu yayin wata ganawa tsakanin ministocin harkokin wajensu a birnin New Delhi

https://p.dw.com/p/125DU
S.M. Krishna, a hagu da Hina Rabbani Khar yayin ganawarsu a New DelhiHoto: dapd

A wata ganawa da suka yi a birnin New Delhi ministocin harkokin wajen Indiya da Pakistan sun yi madallah da abin da suka kira sabon babi na dagantaka tsakanin ƙasashensu. Yayin tattaunawar da ke zaman irinta ta farko, S.M. Kirishna da sabuwar takwararsa ta Pakisan, Hina Rabbani Khar sun daidaita kan yin aiki tare domin yaƙar ta'addacin da kuma bunƙasa ciniki da tafiye tafiye tsakanin ƙasashensu. Yankin Kashmir shi ne ainihin abin dake haifar da rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu. Sau biyu ne dai ɓangarorin biyu suka gwabza yaƙi da juna akan yankin na ƙashmir tun bayan samun 'yancin cin gashin kai a shekara ta 1947.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal