1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Sudan ta Kudu ya yi kamari

Salissou BoukariJuly 10, 2016

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na yin wani zaman gaggawa, domin tattauna halin da ake ciki a Sudan ta Kudu bayan barkewar sabon rikici, a dai-dai lokacin da take cika shekaru biyar da samun 'yanci.

https://p.dw.com/p/1JMdy
Südsudan Juba SPLA-IO Soldaten
Sojoji a birnin Juba na Sudan ta KuduHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Patinkin

Fada dai ya barke tsakanin sojojin da ke biyayya ga shugaban kasar Salva Kiir da kuma na mataimakinsa Riek Machar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 272 cikin kwanaki biyu, akasarinsu sojojin bangarorin biyu da kuma wasu fararen hulla. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya sake yin kira ga shugaban kasar ta Sudan ta Kudu da mataimakinsa da su yi kokarin dakatar da wannan rikici ba tare da bata lokaci ba. Dubban mutane dai na ta fice wa daga birnin na Juba a wannan Lahadi, don gujewa fadace-fadacen na sojoji. Wannan fada dai da ke gudana tun daga ranar Alhamis din makon da ya gabata, na nuni da irin raunin da ke tattare da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.