1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An kira zabe a Japan bayan nada firaminista

Suleiman Babayo JMJ
October 4, 2021

Sabon Firaminista Fumio Kishida na kasar Japan ya kira bayan kasa baki daya a karshen watan Oktoba bayan majalisar dokoki ta tabbatar da shi kan mukamun.

https://p.dw.com/p/41F5v
Japan | Fumio Kishida - Wahl zum Parteivorsitzenden der LDP
Hoto: Carl Court/REUTERS

Majalisar dokokin Japan ta tabbatar da Fumio Kishida a matsayin sabon firamnistan kasar gabanin zaben kasa baki daya na karshen wannan wata na Oktoba. Sabon firaministan ya dauki madafun iko bayan a makon jiya ya zama sabon shugabar jam'iyyar LDP mai mulki inda ya maye gurbin tsohon Firaminista Yoshihide Suga, lokacin da ake samun saukin annobar cutar Covid-19 wadda ta tabarbara lamaru a kasar da ke sahun gaba na kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya.

Shi dai Fumio Kishida mai shekaru 64 da haihuwa ya taba rike mukamun minista harkokin wajen kasar ta Japan kuma a matsayin sabon firamnista yana da jan aikin jagorancin jam'iyyar LDP mai mulki zuwa samun nasara a zaben kasa baki daya da ke tafe ranar 31 ga wannan wata na Oktoba, da farfado da tattalin arzikin kasar da ya samu matsala sakamakon rufe harkoki rayuwa saboda annobar cutar ta coronavirus da duniya ta fsukanta.

Kishida ke zama firamnista na 100 a kasar ta Japan.