Sabon hari kan jami'an tsaro a Nijar
November 20, 2014Gwamnan jihar Tillabery Malam Hasumi Jabiri da wakilinmu na birnin Yamai Gazali Abdu Tessaoua ya tuntuba, ya tabbatar da afkuwar wannan hari. Sai dai har kawo yanzu babu wani bayani dangane da adadin mutanan da suka mutu ko kuma jikkata ta dalilin wannan hari. Bayanai dai na cewa, maharan sun lalata Injiunan kamfanonin sadarwa da ke cikin wannan yanki, wanda hakan ya haddasa tsinkewar layukan salula.
Tuni dai sojojin na Nijar suka yi amfani da jirage masu saukar ungulu na yaki wajan kalubanantar maharan tare da aika wa da karin sojoji a cikin yankin. Dama yau da 'yan makonni da suka gabata, wasu maharan sun hallaka jami'an tsaro guda tara da farar hula biyu, tare da fitar da firsinoni da dama daga gidan kurkuku na garin Wallam da ke cikin wannan jiha.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu