Sabon yunkurin kawo karshen yakin basasar Siriya
October 6, 2013Babban mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen Larabawa a rikicin Siriya, Lakhdar Brahimi, ya jaddada cewar, ba shi da tabbas game da yiwuwar gudanar da taron neman sulhu ga rikicin, kamar yadda kasashen duniya suka tsara yi a birnin Geneva a tsakiyar watan Nuwamban da ke tafe. A lokacin da yake amsa tambayar da tashar telebijin ta TV5 da kuma gidan Rediyon RFI na Faransa suka yi masa, Brahimi ya ce babu tabbas, sai dai kawai yana mika goron gayyata ne kawai ga masu ruwa da tsaki cikin lamarin, kuma yana karfafa musu gwiwar su halarci taron. Dama tun a ranar Talatar (01. 10. 13) da ta gabata ce, Brahimi ya ce ba shi da yakini 100 bisa 100 dangane da yiwuwar taron.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman