Sabuwar barazanar tsagerun Niger-Delta
June 6, 2016Wata sabuwar kungiyar tsagerun yankin Niger-Delta ta yi barazanar kai hare-hare a wasu muhimman wurare a fadin tarayyar Najeriya. Cikin wata sanarwa da ta fitar a Yenagoa fadar gwamnatin Jihar Bayelsa, kungiyar da ke kira kanta Joint Niger-Delta Liberation Force JNDLF a takaice, ta yi ikirarin lalata gine-gine da ta danganta da wadanda gwamnati ta gine da kudaden man fetur da iskar gas da ake tsamowa a yankinsu.
Wuraren da tsagerun suka yi wa barazana sun hada da fadar gwamnatin Najeriyar da ke Abuja, da ma ma'aikatun gwamnati hada da Babban Bankin kasar wato CBN da ke Abuja.
Wannan barazana ta zo ne daidai lokacin da kungiyar Niger-Delta Avengers ke kira ga sauran tsagerun yankin da su hada gwiwa wajen tayar da zaune tsaye a tarayyar Najeriya. Da ma dai harkar fidda danyan mai ya ja baya daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan guda da digo 4 a ko wace rana, sakamakon fashe-fashen bututun mai.