1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dokar aikin jarida a Kenya

November 2, 2013

Shugaban Kenya ya yi alkawarin nazarin dokar aikin jarida da ta haifar da rudani.

https://p.dw.com/p/1AAi6
Hoto: John Muchucha/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kwantar da hankalin 'yan jaridu bisa sabuwar dokar da aka kafa wa kafofin yada labarai, inda ya ce zai tabbatar dokar ta cika sharudan kundin tsarin mulki.

Kafofin yada labarai da 'yan adawa sun soki matakin gwamnatin kasar, tare da cewa sabuwar dokar da 'yan majalisa suka amince da ita, za ta kawo tarnaki kan ayyukan 'yan jaridu a cikin kasar da ke zama mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen gabashin nahiyar Afirka.

Shugaba Kenyatta ya nemi 'yan jarida su nuna sanin dattaku yayin da suke aiki, sannan kuma zai yi nazari sosai kan ayar dokar, wadda sai ya saka hannu a kai kafin ta fara aiki. Sabuwar dokar da ta haifar da mahawarar ta tanadi tara mai tsanani ga duk dan jaridan da ya saba wani bangare na dokar aikin jarida da gwamnatin ta gabatar karkashin wata hukuma.

Tsohon Firaministan kasar ta Kenya Raila Odinga ya nemi gwamnatin kasar ta yi watsi da dokar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman