Sabuwar majalisar kare hakkin dan-Adam
May 9, 2006Jamus dai tana daya daga cikin kasashe na farko da suka bayyana shirinsu na shiga gwagwarmayar neman kujera a sabuwar majalisar ta kare hakkin dan-Adam ta MDD. To sai dai kuma ba tabbas ko kasar zata samu nasara saboda duka-duka kujeru bakwai ne aka ware wa kasashen yammacin Turai kuma wajibi ne kowace kasa ta samu cikakken rinjaye a kuri’ar raba gardama da babbar mashawartar MDD zata kada. To ko ta yaya Jamus zata iya neman goyan baya? Domin kuwa kasar tana da abokan takara masu yawa, wadanda dukkansu ke taimakawa wajen ganin an tabbatar da manufar girmama hakkin dan-Adam. A cikin takardar da ta gabatar ta neman kujerar Jamus tayi nuni da irin gudummawar da take bayarwa game da garambawul ga manufofin MDD sannan a daya bangaren kuma tayi wa MDD alkawarin daukar karin matakai domin tabbatar da hakkin dan-Adam a cikin gida. Bisa ga ra’ayin wakilin gwamnati akan hakkin dan-Adam Günter Nooke shugabancin kasar ta Jamus ga kungiyar tarayyar Turai a watanni shida na farko a shekara mai zuwa abi ne da zai iya taimakawa bisa manufa. Jami’in ya kara da cewar:
Akwai banbancin ra’ayi a tsakanin kasashen Turai, amma babbar hujjarmu ita ce ta shugabancin kungiyar tarayyar Turai shekara mai zuwa. Jami’ai da dama sun amince da haka, musamman ma wadanda ke ba da goyan baya ga gwagwarmayar tamu ta neman kujera a wajen nahiyar Turai.
Fatan Jamus dai shi ne a fara da ita ko da daga bisani bayan wasu ‘yan shekaru zata fita daga majalisar, saboda ba za a yarje wa wata kasa ta shiga majalisar fiye da sau biyu ba. Su kansu kasashe biyar dake da wakilci na dindindin a MDD wajibi ne su tattara nasu ya nasu su fice daga majalisar kare hakkin dan-Adam din bayan shekaru shida. Dukkan kasashen dake da wakilci a majalisar za a rika bitar manufofinsu dangane da hakkin dan-Adam tare da daukar matakai na jan kunne akan duk wata kasar dake neman hana ruwa gudu ga ayyukan kare hakkin dan-Adam na MDD sakamakon manufofinsu na cikin gida, kamar yadda aka saba gani dangane da kasashe irinsu Zimbabwe da China da kuma Sudan. A lokacin da yake bayani Günter Nooke karawa yayi da cewar:
Jamus dai a shirye take ta taka muhimmiyar rawa a wannan bangaren daidai da rawar da ta saba takawa a tsofuwar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD. Kazalika zata yi bakin kokarinta wajen ba da cikakkiyar gudummawa a makonnin farko bayan kama aikin sabuwar majalisar ta kare hakkin dan-Adam domin ganin an dora ta akan wata hanya maidaiciya.