Sabuwar takaddama kan zaben Najeriya
January 14, 2015Majalisar wakilan dai ta dauki matakin amincewa a yi amfani da katin jefa kuri'a na wucin gadi a zaben 2015 maimakon na din-din din da hukumar zaben ke fuskantar matsaloli wajen rarraba shi ga jama'a.
Matsalolin da ke ci gaba da tabaibaye aikin rarraba katin din din din na jefa kuri'ar inda ‘yan Najeriya da dama ke koke har zuwa yanzu ba su kai ga samun katin ba, ya sanya majalisar wakilan Najeriyar daukan wannan mataki, na cewa hukumar zaben ta bar mutane su yi amfani da katin wucin gadi a zaben.
Domin kuwa a yanzu ana sauran wata guda a fara zaben da hukumar zaben Najeriya ta ce mutane milyan 68.8 ne suka cancanci kada kuri'a a sabuwar rijistar da ta fitar, amma milyoyin ‘yan Najeriyar ba su kai ga karaba wannan kati ba.
Duk da dalilai na rashin tsaro da ‘yan majalisar ke ganin na sanya jama'a da dama jan kafa wajen fitowa su karbi katin duk da samar da kasha sabain cikin 100 na katin da aka yi, hukumar zaben Najeriyar na mai jadadda cewa sai mai kati na din din din ne kawai zai iya jefa kuri'a a wannan zabe domin kuwa tana iyakara kokarinta. Mr Nick Dazzan shi ne mataimakin darakta a sashin hulda da jama'a na hukumar zaben Najeriyar.
Sanin cewa an dauki matakai sosai wajen inganta sabon katin zaben wanda ta tantance tambarin ‘yar yatsar hanunun masu jefa kuri'a ne kawai zai sanya a bai wa kowane mutum izinin jefa kuri'a. A yayin da hukumar zaben da majalisar ke jan in ja a kan wannan batu, masharhamnta na kashedin wannan zama wani yunkuri na jikirta zaben da tuni wasu suka fara kiraye–kirayen aikata hakan, musamman saboda rikita-rikitar da ke tattare da zaben na Najeriya.