Safarar mutane zuwa Turai
May 26, 2011'Yan sanda a Jamus sun ce sun kame wasu gungun mutane da ke shigowa da mutane kasashen Turai ta ɓarauniyar hanya. An dai kiyasce cewa a shekaru uku da suka gabata mutane dubu biyu ne waɗannan gungun suka shigo da su Turai ba akan ka'i'da ba. A cewar helkwarar 'yan sandan Jamus d ake birnin Stuttgart, Jamusawa da Turkawa 11 ne mahukunta suka cafke a jihar North Rhine Westaphalia da ta Baden Wuttenberg. A ma watan Fabarairu, sai da mahukuntan Turkiya suka tsare wasu mutane 33 a yankin Istanbul, a matsayin yanki na aikin gano waɗannan gungu. Gungun waɗanda ke da mazauninsu a ƙasar Turkiyya suna amfani ne da manyan motocin ɗaukar kaya wajen dakon mutane. Daga birnin na Istanbul ne kuma jiragen ruwa ke bin da motocin birnin Ahthens na ƙasar Girka zuwa ƙasar Italy da ke zaman mashigi na ƙasashen mambobin Ƙungiyar Tarayyar Turai.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal