Nasara a yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel
September 21, 2021Rundunar ta kungiyar G5 Sahel ta bayyana gamsuwarta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce bayanan da ta samu daga al'umma a yankin Jihar Tillaberi sun ba ta damar cafke gungun wasu 'yan ta'adda a daidai lokacin da suke shirin sayar da wasu gwamman shanu da suka sato.
Sanarwar rundunar ta G5 Sahel ta ce a ranar 12 ga watan nan na Satumba al'ummar gari ta kwarmata wa bataliyar sojojinta 'yan Nijar da ke a girke a yankin Wanzarbe ta gundumar Tera zuwan wasu mutane tara baki da ba su da tabbas a kauyen Baley Koira da ke a nisan kilomita 30 da garin Wanzarbe, suna kore da tarin manyan dabbobi da nufin sayar da su a kasuwar rakumma ta garin.
Karin bayani: Faransa ta sanar da kashe jagoran IS a Sahel
Samamen da sojojin rundunar ta G5 Sahel suka kai a kasuwar bayan samun bayanan ya ba su damar cafke mutanen tara da manyan shanu 18 da kuma sabbin babura. Bayan wannan a ranar 15 ga wannan wata na Satumba a bisa bayanan da suka samu daga al'umma, sojojin rundunar ta G5 Sahel da ke girke a garin Wanzarbe sun yi nasarar kama wani dan leken asirin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasuwar mako-mako ta garin Yatakala. Kuma a halin yanzu an mika gaba dayan mutanen 10 a hannun hukumar yaki da ta'addanci ta kasar Nijar, inda ake can ana ci gaba da yi masu tambayoyi da tatsar bayanai.
Da yake tsokaci kan wannan nasara da sojojin rundunar ta G5 Sahel suka samu Malam Idrissa Maiga jagoran kungiyar kare hakkin al'ummar Jihar Tillaberi ya jinjina wa sojojin da ma talakawan.
To sai wasu kungiyoyin fafutika na ganin akwai bukatar daukar matakin bayar da kariya ga irin wadannan kauyuka, wadanda suka kwarmata wa sojojin labarin 'yan ta'addan.
To amma kuma kungiyar Action For Humanity mai gudanar da ayyukan jin kai a yankin Anzourou na Jihar Tillaberi ta bakin magatakardanta Malam Ibrahim Dambaji ta ce akwai bukatar karin hadin kai da kuma kiyaye hakkin talakawa idan sojojin rundunar ta G5 Sahel na son yin nasara a cikin wannan kokowa.
Karin bayani: Tillaberi: 'Yan majalisa sun koka kan tsaro
Ko a makonni da suka gabata ma dai al'ummomin wasu kauyuka a yankin Zarmaganda sun fitar da tsoro suka fito suka ja daga a gaban wasu maharan 'yan ta'addan da suka yi yunkurin shiga kauyukan nasu har ma suka yi nasarar tilasta masu ranta a cikin na kare.