Sakamakon binciken makaman kasar Siriya
September 14, 2013Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya ce ana sa ran a mako mai zuwa za a bada rahoton da yake tabbabatar da cewa an yi amfani da makamai masu guba a kan fararen hula a yakin da ake ci gaba da gwabzawa a kasar Siriya. A cikin 'yan makwannin ne dai gwamnatin kasar Siriya ta amince da shigar tawagar kwararrun masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya cikin kasar, domin su gudanar da bincike a yankin da ake zargin an yi amfani da makamai masu guba a Damascus babban birini.
A yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniyar ta tabbatar da cewa ta kammala bincike kuma rahoton binciken da aka gudanar ya kammala. Sai dai Sakatare Janar na majalisar ne zai bada takamaiman ranar da za a sanarwa da al'umma sakamakon ba. Ban bai bayyana bangaren dake da alhakin yin amfani da makamai masu gubar ba tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, a harin da aka kai a garin Ghouta dake birnin Damascus a ranar 21 ga watan Augustan da ya gabata.
Maawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe