1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Mulkin Shugaban Gwamnatin Jamus Gerhard Schröder A Tsakanin Shekaru Biyu da Suka Wuce

September 23, 2004

Bayan nasarar zaben shekara ta 2002 shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya gabatar da matakinsa na garambawul mai taken ajenda 2010 kuma a sakamakon haka jam'iyyarsa take fama da bakin jini tsakanin al'umar kasa

https://p.dw.com/p/BvgF
Shugaban gwamnati Schröder
Shugaban gwamnati SchröderHoto: AP

A hakika dai da kyar ne jam’iyyun SPD da the Greens suka tsallake rijiya da baya a zaben da aka gudanar a daidai ranar 22 ga watan satumban shekara ta 2002, inda gaba daya suka tashi da rinjayen kashi 47% a yayinda su kuma ‚yan Christian Union da FDP suka samu goyan baya na kashi 46% na jumullar kuri’u da aka kada. ‚Yan hamayyar ba su yi wata-wata ba wajen korafin cewar gwamnatin Schröder ta tsallake rijiya da baya ne sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta rutsa da wasu yankuna na gabacin Jamus da kuma Allah Waddai da tayi da yakin kasar Iraki. Ita dai gwamnatin Schröder ta fito karara tana mai kalubalantar katsalandan Amurka a kasar Iraki, lamarin dake nuna canjin alkiblar da ba zai taba samuwa ba a karkashin mulkin ‚yan Christian Union. In kuwa har wannan batu na daya daga cikin abubuwan da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar SPD da the Greens a zaben na shekara ta 2002 to kuwa ba shakka wannan wata muhimmiyar alama ce dake nuna wani abin da ya dade yana ci wa jama’a tuwo a kwarya a nan kasar. Abu daya da masu zaben ba su sani ba shi ne kasancewar a cikin ‚yan watanni kalilan bayan haka gwamnatin Schröder zata gabatar da matakanta na garambawul mai taken ajenda 2010. Ainifin manufar gabatar da wadannan matakai kuwa shi ne domin yin gyara ga yawan abin da gwamnati ke kashewa wajen kyautata jin dadin rayuwar jama’a ta la’akari da matsalar rashin aikin yin da ya ki ci ya ki cinyewa. To sai dai kuma kungiyoyin kodago da wasu daga cikin ‚ya’yan jam’iyyar SPD ba su yi wata-wata ba wajen bayyana adawarsu da wannan manufa. Kawo yanzun dai shugaban gwamnati Schröder bai nuna wata damuwa ba yana ci gaba akan bakansa na garambawul bayan da yayi barazanar murabus daga mukaminsa. Amma a daya hannun kuma jam’iyyar SPD tayi asarar da yawa daga magoya bayanta, wadanda suka bijire mata saboda a ganinsu jam’iyyar ta kauce daga shikashikan manufofinta na neman kamanta adalci tsakanin jama’a. Jam’iyyar ta sha kwasar kashinta a hannu a zabubbuka na jihohi da kananan hukumomin da aka gudanar tun daga shekarar ta 2002, ko da yake ita abokiyar hadin guiwarta the Greens dake da hannu a matakan na garambawul kai tsaye da kuma ‚yan Christian Union dake rufa wa gwamnati baya, matsalar ba ta shafe su. Shi dai Schröder yana bin wannan manufa ne saboda sikankancewar da yayi da muhimmancinta dangane da makomar tattalin arzikin Jamus. Kuma muddin hakan ya taimaka aka samu raguwar yawan marasa aikin yi a kasar to kuwa munar masu kalubalantarsa zata koma ciki sannan ya samu kyakkyawar nasara a zabe na gaba da za a yi a shekara ta 2006.