1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon dan wasan Kurket ya kama hanyar zama firamnista

Ramatu Garba Baba SB
July 27, 2018

Sakamakon zaben Pakistan ya nuna cewa kujerun 'yan majalisu 114 daga cikin 269, jam'iyyar Imran Khan ta PTI ta iya samu abin da ke bukatar sai an kafa gwamnatin hadaka bisa rashin rinjaye a majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/32D2v
Pakistan Cricket Kapitän Imran Khan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B.K.Bangash

Kwanaki biyu aka kwashe ana kidayar kuri'un a zaben da masu sa ido kan harkokin siyasa suka ce ba a taba ganin irinsa a shekarun baya bayan nan ba, ganin yadda jama'a suka jure dogon layi don samun damar kada kuri'a duk kuwa da fargabar aukuwar hari irin na ta'addanci da kasar ke fuskanta.

Pakistan | Feiernde Anhänger von Imran Khan 2013
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Arab

Gwarzon tsohon dan wasan Kurket na duniya, Imran Khan da ya lashe zaben, ya yi godiya ga milyoyin magoya baya  inda ya ce nasarar ba ta jam'iyyarsa ta PTI kadai ba ce amma ta mutanen kasa ce baki daya.

Pakistan Charsadda PTI Wahlkampf
Hoto: picture-alliance/Photoshot/S. Ahmad

Sai dai jim kadan da hukumar zaben kasar ECP ta ba da sakamakon, jam'iyya mai mulki ta PML-N, ta yi kalubalanci sakamakon tana mai zargin an tafka magudi. Hukumar zaben ECP ta yi watsi da zargin cewa an tafka magudi a zaben, ta daura alhakin jinkirin da aka samu na bayyana sakamakon zaben a kan wasu matsaloli da suka shafi na'ura.

Rashin samun rinjaye na kujerun 'yan majalisar dokoki na daya daga cikin kalubalen da sabon firaiminstan zai fuskanta.