Sakamakon zaɓen raba gardama a ƙasar Kenya
August 5, 2010Sakamakon wucin gadi na ƙuri'ar raba - gardamar da al'ummar Kenya ta ka'ɗa a jiya Laraba cikin ƙwanciyar hankali,
ya nunar da cewar, ra'ayin 'yan ƙasar ya karkata ne ga sake fasalin tsarin siyasar ƙasar, wadda ke kan gaba wajen ƙarfin tattalin arziƙi a yankin ƙasashen gabashin Afirka.
A cikin sakamakon da hukumomin ƙasar suka wallafa a wannan Alhamis ya nuna cewa kusan kashi 70 cikin ɗari na al Ummar ƙasar
sun goyi bayan samar da sauye sauye ga yadda ake tafiyar da harkokin siyasar ƙasar.
Sauye sauyen dai sun haɗar da rage ƙarfin ikon shugaban ƙasa da ƙara bada fifiko ga shugabanci a yankunan karkara,
kana da warware batun cin hanci da rashawa da kuma matsalar ƙabilanci a ƙasar- matsalolin da kuma ke janyowa ƙasar ta Kenya cikas tun sa'adda ta sami 'yanci daga ƙasar Birtaniya a shekara ta 1963.
Mawallafi : Abdopurahamane Hassane
Edita : Mohammed Awal Nasiru