1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saliyo: Julius Maada Bio ya zama shugaban kasa

Salissou Boukari
April 5, 2018

Rahotanni daga Freetown babban birnin kasar Saliyo na cewa dan takarar babbar jam'iyyar adawa Julius Maada Bio ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da kashi 51.81 cikin 100.

https://p.dw.com/p/2vW0z
Sierra Leone Wahlsieger Julius Maada Bio, neuer Präsident | Amtseid
Hoto: Reuters/O. Acland

Abokin karawar Mr. Bio wato Samura Kamara na jam'iyya mai mulki da ya samu kashi 48.19 a zaben. A cikin daren jiya ne dai shugaban hukumar zaben Mohamed N'Fah Alie Conteh ya sanar da sakamakon inda ya ke cewar "ina mai tabbatar cewa dan takara Julius Maada Bio ya samu kuri'u miliyan daya da dubu 319 da 406 a zaben da ya gudana na 31 ga watan Maris kuma hakan ya bashi damar zama shugaban Jambhuriyar Saliyo."

Bayan sanar da sakamakon zaben, Mr. Bio ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar ta Saliyo batun da ya sanya magoya bayansa barke da sowa bayan da alkalin alkalan kasar Abdulai Charm ya rantsar da shi da mataimakinsa Mohamed Juldeh Jalloh.

Tuni dan takarar jam'iyyar mai mulki ya sanar da aniyarsa ta kalubalantar sakamakon zaben wanda a cewarsa bai gamsu ba sabili da irin konkonton da suke da shi kan sahihancinsa sannan suna zargin cewa an yi aringizon kuri'u, inda ya ce zai garzaya kotu.