1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saliyo: Samura Kamara ya amince da sakamakon zabe

Gazali Abdou Tasawa
April 7, 2018

Dan takarar da ya sha kayi a zaben shugaban kasa da ya gabata a Saliyo Samura Kamara ya amince da shan kaye tare da taya sabon shugaban kasar Julius Maada Bio murna.

https://p.dw.com/p/2vf3i
Sierra Leone Julius Mada Bio Präsidentschaftskandidat
Sabon shugaban kasar Saliyo Sierra Leone Julius MadaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Samura Kamara ya amsa shan kayen ne a gaban 'yan jarida a lokacin wata ziyara da ya kai shi da makarabansa a wannan gidan abokin hamayyar tasa, wanda kuma ke zaman sabon shugaban kasa.

A ranar Larabar da ta gabata Samura Kamara ya sanar da yi wuwar kalubalantar sakamakon zaben. Saidai wannan ziyara da ya kai gidan sabon zababben shugaban, na nuni da cewa ya amince da shan kayen wanda ba kullum ne ta kan kasance haka ba a kasashen Afirka da dama.

Sai dai Samura Kamara ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka dinga muzgunawa magoya bayansa tun bayan bayyana sakamakon zaben, inda ya yi kira ga sabon shugaban da ya dauki matakan kawo karshen hakan. Amma duk da haka ya ce a shirye jam'iyyarsa ta APC ta ke ta kawo goyon bayanta ga sabuwar gwamnatin idan har bukatar hakan ta taso.