Shekaru 20 da kawo karshen yakin basasa a Saliyo
January 18, 2022Kwamitin gaskiya da sansantawa ya duba musabbabin yakin basasar Saliyo, wanda ya haddasa lalacewar ababen more rayuwa da ake da su a kasar. Sannan ya ba da shawarar daukar matakan kawar da rashin adalci da kabilanci da fifikon siyasa da kuma uwa uba cin hanci da rashawa. Sai dai shekaru 20 bayan kawo karshen yakin na basasa, ayar tambaya a nan ita ce: Saliyo ta dauki matakai wajen karfafa zaman lafiya da hadin kan kasa sun sa an samu ci gaba?
Wasu 'yan Saliyo na tattare da kuncin wannan mummunan babi na tarihin kasar. Amma kuma suna ganin cewa ba a magance matsalolin da suka jefa kasar cikin yakin na basasa ba, ballatana ma a dora ta a kan kyakkyawar turba. Theophilus Gbenda, mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya, na daya daga cikin masu wannan ra'ayi.
Karin Bayani:Saliyo: Amfani da yara lokacin yaki
Kusan dai babu wani iyali a Saliyo ba shi da wani labari mai ban tausayi game da yakin basasan kasar da ya gudana tsakanin watan Maris na 1991 zuwa 18 ga Janirun 2002. Daidai da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar na daya daga cikin wadanda abin ya shafa. Dama dai kukumar da yake shugabanta a yanzu na daga cikin shawarwarin da kwamitin sansantawa ya bayar a kafa.
Ra'ayoyi sun zo daya kan cewa Saliyo ta yi kokari wajen gyara kura-kuran da ta tafka, kuma shakka babu ya sa mutane da yawa suna fatan samun ci gaba. Fatmata Kamara 'yar jarida ce kuma ta kasance mai magana da yawun shugaban kasa yayin tattaunawar zaman lafiya a Guinea da Togo. Ta yarda cewa kasar Saliyo tana kan kyakkyawar hanya.
Yakin basasar ya samo asali ne daga wata kungiya mai dauke da makamai da ake kiran kanta RUF, karkashin jagorancin Foday Sankoh. Wannan kungiyar dai tana da kusanci sosai da Charles Taylor, kuma ana kallon yakin basasa da aka yi a Saliyo a matsayin wani ci gaba na abin da ya faru a kasar Laberiya.