1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata sun fita Minna cikin ibadar aikin Hajji a Saudiyya

Yusuf BalaSeptember 22, 2015

Cikin waɗannan masu ibada waɗanda suka isa birnin na Makka sun fara dawafi da kewaye dakin Allah S.W.T cikin ƙasƙantar da kai sanye da farin Ihrami.

https://p.dw.com/p/1Gajb
Beginn Pilgerfahrt Hadsch in Mekka 01.10.2014
Mahajjata a HaramiHoto: Reuters/Muhammad Hamed

Fiye da mutane miliyan biyu ne a ranar Talatan nan suka fita Minna cikin fara aikin Hajji a birnin Makka a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya, taro mafi girma da ke tattara mabiya addinin Islama dan gudanar da ibada wacce ke zama ɗaya cikin biyar na shika-shikan addinin Islama.Cikin waɗannan masu ibada waɗanda suka isa birnin na Makka sun fara dawafi da kewaye dakin Allah S.W.T cikin ƙasƙantar da kai sanye da farin Ihrami abin da ke nuna cewar dukkanin mutane ɗaya suke a gaban wannan ɗaki na Allah ba mai kudi ko mai sarauta.

A gobe Laraba ne kuma ake sa ran ta zama ranar Arafat da ke zama ƙololuwa cikin ranakun Ibadar aikin na Hajjin. A irin wannan rana ta Arafat ce kuma sama da shekaru 1400 Annabi Muhammad S.A.W ya buƙaci haɗin kan Musulmi a faɗin duniya.