Kaddamar da sabon taken Jamhuriyar Nijar
June 22, 2023A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta kaddamar da sabon taken kasar wanda kasar ta samar domin maye gurbin wanda ta gada daga Faransa. Illahirin 'yan majalisar dokokin kasar na bangaren masu mulki da adawa suka kada kuri'ar amincewa da sabon taken bayan yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.
Karin Bayani: Nijar: Mika sabon taken kasa ga majalisa
Sabon taken Jamhuriyar Nijar mai suna "l'Honneur de la Patrie" wanda gwamnatin kasar ta shigar da shi a gaban majalisar dokokin kasar domin samun amincewarta. Da kuri'u 149 ne majalisar dokokin ta kada kuri'ar amincewa da sabon taken wanda ke rubuce a saman shedara 21 da kuma a karanci ke daukar tsawon minti daya da sakonni 41. Assoumana Malam Issa tsohon ministan raya al'adu kana memba a kwamitin rubuta sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar, ya bayyana wasu daga cikin sakonni da sabon taken ke isarwa.
Duk da yake cewa 'yan majalisar dokokin adawa sun kada kuri'ar amincewa da sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar, Honnorable Soumana Sanda na jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka, ya gargadi gwamnati kan cewa sauya take ba wani sauyin da zai haifar ga kasar matsawar gwamnatin ba ta sauya hali ba. 'Yan kasa da dama ne dai suka hallara a zauran majalisar dokokin domin halartar mahawara da kuma kaddamar da sabon taken kasar.
Bayan kaddamar da sabon taken a gaban majalisar dokoki, ba za a soma aiki da shi ba a bainal jama'a sai bayan shugaban kasa ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta haifar da sabon taken nan da makonni biyu masu zuwa.