Kebbi: Matashi mai kera tuka-tuka
June 26, 2019Matashin dai Muhammadu Kabiru da ya kammala karatunsa a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ya ce yanzu haka kusan shekaru tara kenan ya shafe yana gudanar da wannan sana'a ta kera tuka-tukan na gargajiya a kauyensu mai suna Natsini Gada da ke da nisan kilomitoci kalilan daga garin Argungu a jihar Kebbi, lamarin da yasa matsalar ruwa ta kau ga baki dayan kauyen nasu.
Yanzu haka dai wannan matashi ya saukakawa al'umma da dama dangane da magance masu matsalar ruwa a kauyen nasu da ma sauran makwabata. Koda yake matashin ya ce aikin samar da wannan tuka-tukan na gargajiya ba abu ne mai sauki ba, domin ko yana tattare da kalubale irin nashi.
Ba yagama dinbim matasan da ya horar ga wannan sana'a, suma al'ummar gari na cin gajiyar baiwar tasa. DW ta yi nasarar tattaunawa da kadan daga cikin masu gidajen da ke anfanuwa da wannan tuka-tuka na gargajiya. Al'ummar garin na Natsini Gada dai na ci gaba da yabawa wannan matashin kan yadda wannan fasaha tashi ta daukaka wannan gari nasu a idon al'umma.