1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sana'ar wankin motoci bayan kammala jami'a

October 10, 2018

Wani matashi mai suna Nasir da ya kammala karatun jami'a, ya rungumi sana'ar wankin motoci da kuma sayar da kayan abinci ya ce shi kam ba shi da wata bukatar aikin gwamnati.

https://p.dw.com/p/36JqT

Shi dai wannan matashin mai suna Nasir Umar Gummi haifaffen jihar Zamfara da kuma ya kammala digirinsa shekaru biyu da suka gabata a jami'ar Usman Danfodio da ke nan Sakkwato, ya ce dama dai tuni ya dade yana wasu 'yan kananan sanao'i tun kafin ma ya kammala karatunsa a jami'ar, To amma dai matashin ya ce ya dauri aniyar bude wannan kanfanin wankin motocin ne na zamani da kuma samar da kayan makulashe da tande-tande, domin mayar da sana'ar ta zamani da kuma kyautata wa al'umma musamman ma matasa a birnin Sokoto.

Mosambik Straßenhändler in Chimoio
Hoto: DW/B. Jequete

Duk da yake matashin ya ce kanfanin nashi mai suna "Amal Auto Wash and Eatery", du-du-du bai fi shekaru biyu da budewa ba, amma kuma ya samar da gurabun aiki ga dinbin matasa yayin da wasu matasan yanzu haka su ke samun horo. To sai dai matashin ya ce duk da yake ba wani dogon lokaci bane ya share a sana'ar, amma sanadin ta ba karamar riba ya samu ba, inda yanzu hakama yake kokarin bude rassan kamfanin wasu wurare.

Duk da yake matashin yace sana'ar ba karamin kalubale take dashi ba, amma kuma hakan bai sa shi yin kasa a guiwa ba. Wasu matasa da ke aiki a karkashin kamfanin sun bayyana jin dadinsu kan yadda aikin ya taimaki makomar rayuwar su ta hanyar samar musu da wannan aiki da suke yi yanzu.