Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, ta rasu tana da shekaru 96
Sarauniya Elizabeth ta II, ta rasu watanni biyar bayan bikin cikarta shekaru 96 da haihuwa. An shirya mata biki na musamman yayin bikin, inda aka yi harbin igwa daga hasumiyar fadar Hyde Park da ke a birnin London.
1. Lokacin da ta cika shekaru biyu
An haifi Sarauniya Elizabeth II a ranar 21 ga watan Afrilu 1926, amma ba a gudanar da shagulgulan suna ba sai ranar Asabar din farko ta watan Junin wannan shekarar, domin girmama wata tsohuwar al'adar da ta samo asali tun a shekarun 1748 a zamanin Sarki George II.
2. Ba ta taba zuwa makaranta ba
Yara da dama za su so ace ba sa zuwa makaranta, amma daga bisani sarauniya ta ce ba ta jin dadin kin kaita makaranta da aka yi, duk kuwa da malaman da aka dauko mata suna koya mata karatu a gida.
3. Sarauniya na da dangantaka ta jini da mijinta
Marigayi Philip dan uwa ne ga Sarauniya Elizabeth kasanncewar su jikokin Sarauniya Victoria ta II. Elizabeth ta fara nuna soyayyarta ga Yarima Philip tun tana da shekaru 13 da haihuwa, sai dai daga bisani sun auri juna a watan Nuwambar shekarar 1947.
4. Sarauniya na da telanta na musamman
Norman Hartnell (1901-1979) shi ne telan masarautar Ingila a wancan lokacin. Ya dauki lokaci wajen tsara wa Sarauniya Elizabeth rigar da ta sa ranar aurenta da ranar da aka nadata Sarauniya. Wata majiya na cewa, Hartnell ya dinka wa sarauniyar rigunan alfarma kusan takwas.
5. Lu'u-lu'un da aka yi wa hular Sarauniyar ado da shi daga kasar Indiya aka samo shi
Lu'u-lu'un da ake kira "Koh-i-noor" ma'ana hasken duniya a yaran Pasha, ana zargin Turawan mulkin mallaka ne suka sato shi daga masarautar Punjab a Indiya. Kimanin dai lu'u-lu'un guda 108 ne aka kawata hular da su.
6. Ita ce basarakiya mafi dadewa kan karagar mulki
Elizabeth ta zama sarauniya a ranar 6 ga watan Febarairu, 1952 bayan rasuwar mahaifinta Sarki George VI. Yanzu haka ta kwashe shekaru 69 a kan sarauta inda ta zarta kakarta sarauniya Victoria, da ta yi sarauta daga shekara 1837 zuwa 1901 shekaru 63 ke nan.
7. Sarauniyar ba ta bukatar fasfo ko lasisin tuki kamin ta yi tafiya ko tuki
A shafin yanar gizo na masarautar, an rubuta cewa babu bukatar Sarauniya ta mallaki fasfo saboda da ikonta ne ake mallakarsa. A Birtaniya kowa ka iya mallakar fasfo da lasisin tuki ban da Sarauniya ita kadai.
8. Ta kasance mai sha'awar kananan karnuka
Karnuka na samun kulawa a kasashen Turai. Sai dai karen Sarauniya ya zarta tsara, Sarauniya Elizabeth ta fara sha'awar kananan karnuka tun a shekarun 1930 da mahaifinta ya yi mata kyautar wani kare da take kira Dookie. Amma wanda ta fi so a rayuwarta wani ne da ake kira Susan.
9. An kwaikwayi surar Sarauniya a cikin fina-finai sama da 100
Kimanin fina-finan tarihi da na nishadantarwa sama 225 ne aka yi amfanin da surar Sarauniya wanda ya bata damar lashe kyautar BAFTA a shekarar 2013. Hoton da kuke gani a sama wata 'yar fim ce mai suna Claire Foy da ta yi shigar Sarauniya, a cikin fim din "The Crown"
10. Akwai mutanen da suka fi Sarauniya kudi a Birtaniya
An ruwaito a mujallar Forbes cewa Sarauniya ta mallaki dukiya da adaddinta ya kai Pan miliyan 350, wanda idan aka hada shi da abin da sarkin yankin Westminister Earl Grosvenor ya mallaka ba wani abu ba ne, wanda ya mallaki Pan biliyan 10. Elizabeth ta kasance ta 372 a jerin mutane dubu masu kudi a Birtaniya.
Liyafar cika shekaru 70 kan gadon sarauta
A ranar 6 ga watan Fabrairu, 2022, sarauniyar ta yi bikin cika shekaru 70 kan gadon sarauta. Za a kwashe tsawon shekarar ana gudanar da bukukuwa, da kololuwarsu za su kasance daga 2-5 ga watan Yuni. Sarauniya Elizabeth ta biyu dai, ita ce sarauniya mafi tsufa a duniya.