1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Charles III ya ziyarci majalisar Birtaniya

Binta Aliyu Zurmi
September 12, 2022

Sarki Charles III ya gode wa 'yan majalisar bisa ta'aziyyar mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth II a ziyararsa ta farko ga majalisar dokokin Birtaniya

https://p.dw.com/p/4Gjt1
England London | Westminster Hall | King Charles III.
Hoto: HENRY NICHOLLS/AFP/Getty Images

Da yake jawabi yayin ziyarar mai cike da tarihi, sarkin ya sha alwashin ci gaba da mutunta majalisar da ma al'adun masarautar Birtaniya kamar yadda mahaifiyarsa ta yi a lokacin da ta ke raye.

Jim kadan bayan kammala jawabinsa da ma karba ta'aziyyar a zauren taro na Westminster, Sarki Charles III da mai dakinsa sun kama hanyar Edinburgh da ke yankin Scotland inda gawar Sarauniya ta ke wadda za a kai majami'ar St. Giles domin al'umma su sami damar yi mata bankwana.

A ranar Litinin din 19 ga watan Satumba za a binne Sarauniya Elizabeth II a makabartar da ke fadar Windsor kusa da mijinta wanda ya rasu a 2021